An yi karar Facebook bisa leken asiri

Fiye da mutane miliyan 500 ke amfani da Facebook.
Facebook na fuskantar wata karar hadaka game da zargin ya na sa ido kan sakonnin sirrin da masu amfani da shafin ke aikewa.
Masu shigar da karar sun ce Facebook na lalubar sakonnin da masu amfani da shafin ke aikawa domin tattara bayanai da mika su ga kamfanonin kasuwanci da tallace-tallace.
Sai dai Facebook ya musanta zargin.
Kakakin kamfanin ya ce; "Zamu kare kanmu bakin iyawarmu."
Masu karar na neman Facebook ya biya tarar $100 a kullum ga masu amfani da shafin ko kuma $10,000 a dunkule ga duk mai amfani da shafin.
Karar da aka shigar cikin makon jiya, ta kafa hujja da wani bincike mai zaman kansa da ta ce, ya gano cewa Facebook na nazarin sakonnin da ake aikewa ta shafin "saboda dalilan da ba su shafi aikewa da sakonnin ba."
Damar cin riba

Makirkirin Facebook Mark Zuckerberg ya musanta zargin.
Karar ta ce; "Nuna wa masu amfani da shafin cewa sakonnin da suke aike wa na sirri ne wata damar cin riba ce ga Facebook."
Ta ce: "Hakan na faruwa ne kuwa saboda masu amfani da Facebook za su saki jiki su bayyana wasu abubuwan sirri cikin sakonninsu da ba za su baiyana ba idan sun san cewa akwai masu sa ido a kai."
"Don haka Facebook zai samu bayanan da zai sayar ga masu bukata ba tare da amincewa ko ma sanin masu amfani da shafin ba."
Sai dai kuma wasu mutanen sun fara kare Facebook game da tuhumar.
Kwararre kan harkar tsaro, Graham Cluley ya ce idan shafin ba ya lura da sakonnin da ake aikawa ta sirri, Facebook zai yi sakaci da aikinsa na kula da masu amfani da shi."
Ya ce; "Idan ba'a nazari tare da binciken sakonnin da ake aikewa akwai yiwuwar wasu su yi amfani da damar wurin aikewa da sakonnin da ke dauke da manhajar kwamfuta mai leken asiri ko kuma lalata bayanan da aka adana."
Suka
A baya dai Facebook ya sha suka kan tsarinsa na tsare sirrin masu amfani da shi.
A Satumban bara, shafin ya sha suka game da yunkurin sauyin manufofin sirrin ta yadda za'a iya ba da damar kirkirar tallace-tallace ta hanyar amfani da sunaye da kuma hotunan masu amfani da shafin.
Kamfanin ya ce kudirin na sa ya yi warawara da manufar sirrinta bayanan shafin ne ba wai sauya wa ba.
Facebook ya amince da sauya kalmomin manufar ne bayan wata kara da aka kai kamfanin a 2011 wacce ta sa shi biyan tarar $20 miliyan ga masu amfani da shafin da suka yi zargin ya yi amfani da bayanansu ba tare da izininsu ba.