MINT: Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa

Image caption Tattalin arzikin Nigeria na samun tagomashi.

Kwararren masanin tattalin arzikin nan Jim O'Neil na ganin Najeriya na gaba-gaba a cikin kasashen da tattalin arzikinsu zai bunkasa.

Masanin ya ce rukunin kasashen da ya kira "Mint" wato Mexico, Indonesia, Nigeria da Turkey na da wasu tubalai na bunkasar tattalin arziki.

Tubalan dai sun hadar da yawan al'umma, dimbin matasa masu jini a jika, da kuma kasuwanni da za su iya sayar da kayayyakinsu a cikin gida da waje.

Sai dai a gefe daya kuma Nigeria na fuskantar kalubale, da ya hadar da cin hanci da rashawa, basussuka, rashin shugabanci na gari, rashin abubuwan more rayuwa da kuma tabarbarewar ilmi.

Karin bayani