An fitar da taragon farko na makaman Syria

Image caption Kokarin lalata makaman Syria

An fitar taragon farko na makaman Syria masu guba daga kasar a cikin shirin kasashen duniya na lalata makaman Shugaba Bashar al-Assad.

Masu sa'ido daga hukumar haramta makamai masu guba sun ce an dora kwantenoni tara na makaman a cikin wani jirgin ruwa na kasar Denmark a tashar ruwan Latakia na Syria don fitar dasu waje.

Dakarun ruwan Rasha dana China ne suka yi wa jirgin ruwan rakiya

Shugaba Assad ya amince a lalata makamansa tun a bara bayanda ya fuskanci matsin lamba daga kasashen waje a kan cewar ya yi amfani da makami mai guba a kan fararen hula a Damascus.

Matakin da yasa kasar ta kaucewa yaki da kasar Amurka.

Karin bayani