An amince a sake shari'ar soji a Turkiyya

Image caption Akwai yiuwawar a sake shari'ar sojojin da aka tuhuma da hmbara da mulkin Erdogan

Pirai ministan Turkey Recep Tayyep Erdogan ya amince a sake shari'a ga jami'an soji da a baya aka zarga da hambarar da mulkinsa.

A baya dai babban mai ba shi shawara ya ce 'yan sanda da masu shigar da kara sun shiryawa jami'an sojin gadar zare.

A watan Disambar bara ne masu shigar da karar suka sa aka kame wasu daga cikin abokan Mr Erdogan da aka tuhume su da laifin cin hanci da rashawa.

Wakilin BBC a birnin Santambul ya ce wannan sabon jawabi na Mr Erdogan ya nuna cewa a yanzu ya na goyon bayan bangaren sojojin kasar masu raba siyasa da addini wadanda yake adawa da su a baya.

Karin bayani