Ana muku-mukun sanyi a Amurka

Image caption Dusar kankara da sanyi na karuwa a Amurka

Iska mai sanyin gaske ta yankin Arctic ta fara ratsawa ta tsakiyar yammacin kasar Amurka.

Yanzu haka sanyin ya tsananta inda hakan ka iya barazana ga rayuwar al'umma.

Hukumomi sun ce Amurkawa da dama ba su taba fuskantar irin wannan muku-mukun sanyin ba.

Magajin garin Indianapolis a jihar Indiana Greg Ballard ya shaidawa BBC cewa "Wannan yanayin da ake ciki na tsananin sanyi hade da dusar kankara bamu taba ganin irin sa ba a shekaru fiye da 10 a wannan yankin."

Karin bayani