ISIS ta nemi goyon bayan kabilu a Iraqi

Image caption Masu tada kayar baya na jan hankalin kabilu 'yan sunni a Iraqi

Masu tada kayar baya a garin Fallujah a yammacin Iraqi sun yi kira ga kabilu 'yan sunni a yankunan da su mara musu baya a rikicin da suke yi da gwamnatin Iraqi mai bin akidar Shi'a.

Sun kuma yi kira ga iyalan da suka bar muhallinsu don jin tsoron rikicin da su dawo gidajensu.

Wannan kiran da masu tada kayar bayan suka yi ya zo ne bayan da gwamnatin kasar ta yi kira ga 'yan yankin Fallujah da su kori masu tada kayar bayan.

Masu tada kayar bayan dai na son amfani da kin jinin gwamnatin 'yan Shia da 'yan sunni ke yi don samun goyon baya da kara fadada.

Ita kuma gwamnatin kasar na son razana mazauna birni don su yaki masu tada kayar bayan ko sa sami kubuta daga harin da gwamnati ke kaiwa yankin.

Karin bayani