Ta yiwu a tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Image caption Yakin Sudan ta Kudu ya rutsa da dubunnan farar hula.

Wakilan gwamnatin Sudan ta Kudu da kuma tsagin rundunar sojin kasar da su ka yi tawaye sun fara tattauna batun tsagaita wuta.

Ministan sadarwa Michael Makuei ya ce an kuma tabo batun fursunonin siyasa.

Bangarorin biyu dai sun bayyana bukatar dakatar da rikicin, sai dai gwamnati ta ce dakarunta na ci gaba da kai hari kan garin Bor.

Biyu daga cikin masu tattaunawar sun bar Ethiopia domin ganawa da shugaba Salva Kiir a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu.

Karin bayani