Tattaunawa kan kawo karshen rikicin CAR

Image caption Rikicin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya na kara kazanta

A yau ne za'a fara wani taro a kasar Chadi don tattauna hanyoyin daya kamata a bi, don kawo karshen rikicin da ake fama da shi a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Ana saran shugabannin Kasashen yankin ne dai zasu halarci taron.

Tuni dai shugaban kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiyar Michel Djotodia ya isa Njamena, babban birnin kasar Chadi don halartar taron.

Taron na zuwa ne yayin da Asusun kula da kananan yara na Majalisar dinkin duniya wato UNICEF ya yi kashedin cewa, Jamhuriyyar Afrika ta tsakiyar na gab da fadawa wani bala'ain da ya shafi jama'a.

Farfesa Bube Namaiwa, malami ne a jami'ar Sheikh Anti Diop dake kasar Senegal kuma ya fadawa BBC cewa ba za a sami biyan bukatar da ake so ba har sai Kasashen Turai irinsu Faransa sun shiga tattaunawar.

Karin bayani