An kai hari a wani Masallaci a Kwankwaso

Image caption An kai harin ne masallacin mahaifin gwamnan Kano

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukan su sakamakon wani hari da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai a wani masallaci dake garin Kwankwaso a jihar Kano.

Wasu mutanen kuma sama da 10 sun ji raunuka ciki har da yara kanana.

Lamarin dai ya faru ne a masallacin kofar gidan Hakimin Madobi wanda kuma mahaifi ne ga gwamnan Kano a dai dai lokacin da ake sallar Isha'i a ranar Talata.

Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da afkuwar lamarin amma ba ta bada cikakken bayani ba kawo yanzu.

Karin bayani