An nemi shugaban CAR ya sauka

Image caption Michael Djotodia ya ce ba zai sauka daga shugabancin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ba.

Shugabannin kasashen Afrika na tattaunawa a Chad game da rikicin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Shugaban kasar na rikon kwarya Michel Djotodia na fuskantar matsi kan ya sauka daga mukaminsa saboda kasa tsayar da fadan da ya barke tsakanin 'yan bindiga Kirista da Musulmi, sai dai kakakinsa ya shaida wa BBC cewa ba zai sauka ba.

Kusan rabin mazaunan Bangui, babban birnin kasar sun tsere wa yakin, inda mafi yawansu ke fakewa a sansanin dakarun Faransa da ke filin jiragen saman kasar.

Mr Djotodia ya karbi ragamar iko ne sakamakon juyin mulki a watan Maris din da ya gabata, abin da ya jefa kasar cikin rikici.

Karin bayani