Za'a gwada motar lantarki ta haya a UK

Image caption Motar za ta yi caji ne idan ta rabi faifan caji ba tare da jona wa ba.

Za'a fara gwajin motocin haya da za su yini su na aiki da wutar lantarki a Ingila.

A cikin watan Janairun nan ne wasu sababbin motoci guda takwas masu aiki da wutar lantarki za su fara aiki a garin Milton Keynes.

Motocin za su jima su na aiki ne saboda za su rika samun cajin batirinsu a tashoshin farko da na karshe a hanyarsu ta hanyar wasu fayafayan caji da aka manna kan kwalta.

Wannan karo na farko a fadin UK da za'a yi amfani da irin wadannan motoci.

Cajin rabe

Motocin dai za su rinka zirga-zirga ne kan wata hanya mai nisan kilomita 25 tsakanin unguwannin Wolverton da Bletchley na garin Milton Keynes inda za su dau fasinja 800,000 kowacce shekara.

Bayan caji da daddare a tasha, motocin za su rinka caji a farko da karshen hanyar.

Motocin za su rinka tsayawa ne kan wasu fayafayan caji da aka manna kan kwalta. Daga nan direban zai saukar da wani faifai da ke kasar motar wanda zai karbi cajin. Cikin mintuna 10 motar ta koma bakin aiki.

Wannan tsarin na rashin ta hanyar rabe maimakon joni zai taimaka wurin caja batirin motar cikin hanzari.

A kan yi haka

Tuni dai aka fara amfani da irin wannan tsarin cajin a garuruwan Turin da Genoa na Italy, Utrecht na Netherlands da Mannheim a Jamus.

A bara, an bude wata hanya a Koriya ta Kudu mai nisan kilomita 12 wacce ke caja batirin motoci masu amfani da wutar lantarki ba tare da sun tsaya ba. A garin Gumi dake kasar kuma akwai motocin haya biyu da ke amfani da wutar lantarki.