Za a saki 'yan Boko Haram 167

Image caption Ana zargin cewa an kashe daruruwan wadanda aka tsare

Rundunar sojin Nigeria ta ce za ta saki 'ya'yan kungiyar Ahlussunah Lidda'awati wal jihad da aka fi sani Boko Haram guda 167 wadanda aka kama lokacin da aka kai samame a wurare daban-daban a arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da kakakin sojin, Manjo Janar Chris Olukolade, ya fitar ya bayyana shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ne ya yi wa 'ya'yan kungiyar afuwa don haka ya ba da umarni a sake su daga wuraren da ake tsare da su a jihohi uku na arewa maso gabashin kasar.

Kazalika kakakin sojin ya ce za a saki mutanen ne bayan da wani kwamitin bincike ya ba da shawarar sakinsu.

Gwamnatin Nigeria dai ta ki ba da amsa game da zargin da ake yi cewa an batar da daruruwan 'ya'yan kungiyar Boko Haram din da ake tsare da su ko ma an kashe su.

Karin bayani