Shugaban kasar CAR ya sauka daga mulki

Image caption Michel Djotodia ya sauka daga mulki don sasanta rikicin CAR

Shugaban jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Michel Djotodia ya sauka daga mukaminsa.

Mr Djotodia ya ajiye mukaminsa ne a taron shugabannin kasashen tsakiyar Afrika a kasar Chad.

An dai zarge shi da gaza kawo karshen rikici tsakanin Kirista da 'yan tawayen da mafi yawansu Musulmi ne wadanda suka dora shi kan shugabanci bayan wani juyin mulki a bara.