Shugaba Michel Djotodia ya yi murabus

Image caption Michel Djotodia lokacin da yake shan rantsuwa

Shugaban riko na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Michel Djotodia ya yi murabus bayan makwanni da aka shafe ana tashin hankali mai nasaba da addinni a cikin kasarsa.

Mr Djotodia ya ajiye mukaminsa ne a taron shugabannin kasashen tsakiyar Afrika a kasar Chad.

An dai zarge shi da gaza kawo karshen rikici tsakanin Kirista da 'yan tawayen da mafi yawansu Musulmi ne wadanda suka dora shi kan shugabanci bayan wani juyin mulki a bara.