An sasanta rikicin Jonathan da Sanusi

Image caption Shugaba Jonathan da Sanusi Lamido Sanusi

Rahotanni a Nigeria sun ce wasu dattawa a kasar sun sasanta rashin fahimtar juna da ta kunno kai tsakanin Shugaban kasa, Goodluck Jonathan da kuma Gwamnan babban bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi.

Wadanda su ka shiga tsakani dai na ganin idan har ba a sasanta ba, rashin jituwar na iya tasiri a kan tattalin arzikin kasar.

Wasu majiyoyi a babban bankin Nijeriyar, sun ce bayan shiga tsakanin, Shugaba Jonathan ya amince Gwamnan babban bankin ya ci gaba da rike mukaminsa har sai ya cika wa'adin aikinsa.

A baya dai Mr Jonathan dai ya bukaci Sanusi Lamido Sanusi da ya yi murabus daga kan mukaminsa nan take, bisa zargin shi ne ya tesgunta wasikar da ya rubuta, inda ya yi ikirarin cewar kamfanin NNPC bai bayyana yadda ya yi da dala biliyan 49.8 ta kudaden danyen mai ba.

Gwamnan babban bankin ya shaidawa Shugaban kasar cewa ba zai yi murabus ba kuma zai tsaya har sai karshen wa'adin da dokar kasa ta tanadar masa.

A na ta bangaren, jam'iyyar adawa ta APC ta bukaci Shugaban Najeriyar ya ciza ya hura a kan wannan takun saka, saboda hakan zai iya yin illa ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

Karin bayani