Kenya ta kashe mayaka 30 a Somalia

Image caption Dakarun al-Shabaab na iko da kudanci da tsakiyar Somalia

Kenya ta ce ta kai harin sama kan wani sansanin masu kishin Islama a Somalia, inda ta kashe mayaka 30, ciki har da kwamandojin al-Shabaab.

An kai harin ne a Garbarahey, kusa da iyakar Kenya da Ethiopia.

Kafafen yada labaran kasar sun ce mutane 10 aka kashe koda yake mazauna yankin sun ce an rusa gine-gine da dama.

Kenya dai ta na da dubunnan dakaru a Somalia da ke taimakawa gwamnatin da ke samun goyon bayan Majlaisar Dinkin Duniya wurin yaki da al-Shabab, mai alaka da al-Qaeda.