Za a kwashe 'yan ci rani 33,000 daga CAR

Image caption 'Yan ci rani 33,000 ne rikicin CAR ya rutsa da su

A yau Asabar ne wata Kungiyar Kasa da Kasa dake kula da masu yawan cirani zata soma kwashe kashin farko na dubban baki 'yan Kasashen wajen da rikicin Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya ya rutsa da su.

Kungiyar kula da 'yan ciranin ta ce 'yan Afirka kusan 33,000 ne daga kasashen dake makwabtaka ke rayuwa a wani yanayi mara dadi, kuma suke bukatar barin jamhuriyyar Afirka ta Tsakiyar.

Kusan mutum miliyan guda suka rasa matsugunansu saboda fadan da aka shafe watannni ana yi tsakanin 'yan bindiga musulmi da kuma Kirista.

A ranar jumua'a ne dai Shugaban Kasar musulmi na farko Mishal Djotodia ya sauka daga kan kujerarsa bayan ya sha matsin lamba a wata ganawa da aka yi ta shugabannin Kasashen yankin a Chadi.

Labarin saukar tasa, ya janyo shagulgula da raye raye a yankunan da Kiristoci suke.

Karin bayani