Ana alhinin rasuwar Ariel Sharon

Ana ci gaba da nuna alhini dangane da mutuwar tsohon Praministan Isra'ila, Ariel Sharon wanda ya mutu yana dan shekaru tamanin da biyar bayan ya kasance cikin dogon suma tun shekara ta 2006.

Sharon dai ya kamu da cutar bugun jini kafin ya shiga dogon suma.

Praministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce, Sharon zai ci gaba da kasancewa har abada a zukatan al'ummar kasar.

Amma ƙusa a kungiyar Palasdinawa, Dr Mustafa Barghouti ya ce, su dai a wurinsu babu wani abin kirki da Sharon ya yi a rayuwarsa.