Amurka ta yi tur da Nigeria kan auren jinsi guda

Image caption 'Yan luwadi da madigo za su fuskanci dauri a Nigeria

Gwamnatin Amurka ta yi tur da matakin da Nigeria ta dauka na sanya hannu kan dokar da ta hana auren jinsi guda a kasar.

A wata sanar da Sakataren wajen Amurka, John Kerry, ya fitar ya ce hakan tauye hakkin bil adama ne.

Mista Keri ya kara da cewa Nigeria ta sabawa dokar kasashen duniya wacce ta bai wa kowa damar gudanar da rayuwar da yake so ba tare da tsangwama ba.

Shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya rattaba hannu kan dokar da ta haramta aure tsakanin jinsi guda bayan da majalisun dokokin kasar su ka zartar da ita.

Daurin shekaru 10 ga wanda ya taimaki 'yan luwadi da madigo

Dokar dai ta tanadi daurin shekaru 14 ga duk 'yan luwadi da madigon da su ka auri junansu.

Haka kuma ta tanadi daurin shekaru 10 ga duk wanda ya taimaka irin wannan auren ya tabbata.

Luwadi da madigo dai ya saba wa manyan addini da al'adun al'ummomin Nigeria.

Sai dai masu rajin kare hakkin bil'adama na ganin hakan keta hakkin masu wannan dabi'ar ne.

Karin bayani