'Yan adawa na zanga zanga a Bangkok

Image caption Zanga-zangar kin jinin gwamnati na ruruwa a Thailand

'Yan adawa masu zanga zanga a Thailand sun rufe mahadar tituna da dama a birnin Bangkok, a wani bangare na ganin sun hanbarar da gwamnati kafin zabubbukan da za'a gudanar a ranar 2 ga Fabrairu.

Gwamnatin Thailand ta jibge 'yan sanda da sojoji 18,000 ta kuma saka karin jami'an tsaron a cikin jiragen kasa domin ganin cewa ma'aikata sun je wuraren aikinsu.

Masu zanga zangar dai sun gina shingaye, kuma sun rufe tituna da dama.

Hukumar zabe a yanzu ta nemi gwamnati da ta dage zabukan zuwa watanni uku, saboda halin da ake ciki na tsaro.

Amma wani mataimakin Pirai ministan Thailand ya shaida wa BBC cewa hakan ba zai yiwu ba.

Masu zanga zangar sun zargi Pirai minista Yingluck Shinwat, da yi wa dan uwanta aiki, wanda aka kora a shekarar 2006.

Karin bayani