Sarkin Dubai ya bukaci a sararawa Iran

Image caption Sheikh Mohammed al-Maktoum

Fira Ministan hadaddiyar daular Larabawa, Sheikh Mohammed Al-Maktoum ya shaidawa BBC cewar ya kamata yanzu ya cire takunkumin karya tattalin arzikin kasar da aka sanyawa Iran.

Daga ranar litinin mai zuwa dai kasashen duniya zasu sassauta takunkumin da aka sanyawa Iran din, bayan da aka daddale akan wata yarjejjeniya kan shirin nukiliya na Iran.

To amma Sarkin Dubai, Sheikh Mohammed Bin Rashid Al-Maktoum, ya ce kowa zai amfana idan aka sararawa kasar ta Iran.

Yace "Iran makwabciyar ce. Bama son wani tsahin hankali, kuma suma suna son zaman lafiya. Idan suka fahimci juna da Amurka har aka dage takunkumin da aka sanya masu kowa zai anfana. Muma mun ji radadin takunkunmin".

Dubai ta na da hulda ta kut da kut da Iran, domin akasarin harkokin kasuwancin da ake yi da kasar Iran suna bi ne ta hadaddiyar daular larabawan.

Karin bayani