Ana zaben raba gardama a Masar

Image caption Zaben raba gardama a Masar na jan hankali

Al'ummar Masar na kada kuri'a kan daftarin tsarin mulkin kasar, inda gwamnati ke gargadin daukar matakin kar-ta-kwana kan duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaben na kwanaki biyu.

Ana shirya kundin ne domin maye gurbin tsarin mulkin da shugaban kasa mai kishin Islama, Muhammad Morsi ya kaddamar kafin sojoji su hambarar da mulkinsa a watan Yuli.

Kungiyar 'yan uwa Musulmi, wacce sojojin suka haramta suka kuma kira ta 'yar ta'adda ta nemi a kaurace wa kada kuri'ar.

Sabon tsarin mulkin dai ya haramta jam'iyyu masu akidar addini, ya bunkasa hakkin mata, amma ya kara tabbatar da karfin soji cikin mulkin Masar.

Karin bayani