India ta yi sallama da Polio

Image caption Nigeria, Afghanistan da Pakistan ne kawai ke fama da Polio a duniya.

India ta cika shekaru uku ba'a sami wanda ya kamu da Polio ba, abinda zai share hanyar tabbatar da cewa ta yi sallama da cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce idan ta tabbatar babu sauran mai Polio a India, za ta bayyana kasar a matsayin inda aka kawar da cutar cikin Maris mai zuwa.

Tun tsakiyar shekarun 1990 ne India ke gudanar da gangamin rigakafin cutar Polio inda fiye da 'yan sa-kai miliyan biyu ke gudanar da aikin.

A watan Janairun 2011 ne aka samu yaro na karshe da ya kamu da Polio a jihar West Bengal.

Kasashen Afghanistan, Pakistan da Nigeria ne kadai ake ci gaba da samun cutar Polio a fadin duniya.

Karin bayani