Nigeria: 'Sanatoci 17 za su bar PDP'

Image caption Shugaban PDP Alhaji Bamanga Tukur.

A Najeriya, sanatoci 17 da aka zaba a jam'iyyar PDP mai mulkin kasar na shirin koma wa jam'iyyar adawa ta APC bayan da gwamnoni da 'yan majalisar wakilai su ka koma.

Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawan kasar, Alhaji Bindo Umaru Jibrilla ya shaida wa BBC cewa za su sauya shekar ne da zarar majalisa ta koma bakin aiki.

Sanata Jibrilla ya ce rashin adalci ne ya sa za su sauya sheka daga jam'iyyar ta PDP.

Tuni dai gwamnoni biyar da 'yan majalisar wakilai 37 su ka sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC a shirye-shiryen da 'yan siyasar kasar ke yi na tunkarar zabubbukan 2015.

Karin bayani