Rikici ya barke a APC Gombe

Image caption APC na fama da rikicin shugabanci tsakanin 'yan sabuwar PDP da 'yan rusassun jam'iyyun ACN, ANPP, da CPC.

A Nigeria rigimar shugabanci ta barke a reshen jam'iyyar adawa ta APC da ke jihar Gombe a arewacin kasar.

Rikicin ya biyo kafa kwamitin shugabancin rikon kwarya inda na hannun daman tsohon gwamna Danjuma Goje na jam'iyyar PDP, Barista Magaji Daho ya zamo shugaba.

Ana dai sa ran tsohon gwamna Danjuma Goje na cikin sanatocin da za su sauya sheka zuwa jam'iyyar da zarar majalisar dattawan Nigeria ta koma bakin aiki.

Sauran 'yan jam'iyyar daga rusassun jam'iyyun ACN, ANPP da CPC na ganin hakan rashin adalci ne.

Mutumin da ya yi wa jam'iyyar CPC takarar gwamna a zaben 2011 Alhaji Abubakar Aliyu ya ce za su nemi bahasi daga uwar jam'iyya kuma idan ba su gamsu ba za su bayyana matakin da za su dauka.

Sabuwar jam'iyyar ta APC dai na fama da irin wannan rikicin shugabanci tsakanin 'yan jam'iyyu ukun da su ka fara kafa ta da 'yan tsagin sabuwar jam'iyyar da suka shiga jam'iyyar musamman a jihohin Adamawa, Kano da Sokoto.

Karin bayani