Sojin sama sun kai wa Sanata Ndume hari

Image caption Sanata Ali Ndume na zargin soji da kashe farar hula bisa kuskure

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawan Nigeria, Ali Ndume ya ce ya tsallake rijiya da baya lokacin da jiragen yaki suka bude wa tawagarsa wuta a yankin Gwoza da ke jihar Borno.

Ali Ndume ya shaida wa manema labarai cewa sojojin saman Nigeria sun kai wa tawagarsa hari ne bisa kuskure, inda su ka yi tsammanin mayakan Jama'atu Ahlis Sunnah lid da'awati wal jihad, da aka fi sani da Boko Haram ne ke wuce wa.

Ya ce hakan ya nuna cewa sojojin sun sha hallaka farar hula ke nan da sunan 'yan Boko Haram ne.

Rundunar sojin saman Nigeria ta tabbatar da kuskuren amma ba ta mai da martani kan zargin kashe 'yan ba-ruwana ba.

Karin bayani