An nemi 'yan adawar Syria su shiga sulhu

Image caption 'Yan adawa a Syria na fuskantar barazanar janyewar tallafi

Wani babban jami'i na 'yan adawa a Syria ya ce gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun yi gargadin cewa za su sake nazari kan irin taimakon da suke bai wa gamayyar 'yan adawar matukar suka ki halartar taron sulhu don warware rikicin kasar da aka shirya gudanarwa a Geneva a mako mai zuwa.

Wadannan kalamai dai sun kara nuna irin matsin lamba ta bayan fage da ake yiwa 'yan adawar dake shirin kada kuri'a game da batun a ranar Juma'a mai zuwa.

Wakilin BBC ta fuskar diplomasiyya ya ce matukar 'yan adawar suka ki halartar wannan taron, dabarar cewa a yi dogaro da diplomasiyya wajen kawo karshen rikicin ka iya wargajewa.

Amma dai a bayyane take jan hankalin 'yan adawar su amince su yi gaba da gaba da gwamnatin Shugaba Assad ya na da dan karan wahala.

Karin bayani