Hollande: 'Ina fuskantar matsala a rayuwa'

Shugaba Francois Hollande Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Hollande ya amince yana fuskantar matsala a rayuwarsa

Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya ki ya fito fili ya bayyana cewa ko har yanzu Valerie Trierweiler ce abokiyar zamansa.

A taron manema labaransa na farko tun bayan da wata mujalla ta zarge shi da yin lalata da wata mata mai fitowa a fina-finai, Mr Hollande ya amince cewa, yana fuskantar matsala a rayuwarsa, to amma ya ce a gida ya kamata a warware duk wata matsalar da ta shafi rayuwar mutum, ba a kasuwa ba.

Shugaba Hollande ya yi alkawarin kawo karin haske kafin ziyarar da zai kai Amirka a watan gobe, inda ake sa ran zai tafi tare da abokiyar zaman tasa Valerie.

Amma a yanzu tana can kwance a asibiti, saboda ta girgizu da jin ya ci amanarta.

Kafin a yi masa tambaya a kan zargin, Mr Hollande ya yi bayani kan wasu sabbin manufofi da gwamnatinsa ta bullo da su da nufin farfado da tattalin arzikin Faransa, wadanda suka hada da rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa da kuma kara yawan guraben aikin yi.

Karin bayani