Bam ya tashi a wata kasuwa a Maiduguri

Jihar Borno na karkashin dokar ta baci

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Jihar Borno na karkashin dokar ta baci

Rundunar sojin Nigeria ta ce bam ya tashi a kasuwar Jagwal dake tsakiyar Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Lamarin dai ya janyo rasuwar mutane da dama da kuma jikkatan wasu.

Wani wanda ya ce a kusa da inda yake sana'a bam din ya tashi ya shaida wa BBC cewar bam din ya tashi ne jim kadan bayan da wata 'keke napep' ta shiga cikin kasuwar.

Wasu rahotanni sun nuna cewar, wani dan kunar bakin wake ne ya tada bam din kusa da wajen binciken ababen hawa na sojoji a Maidugurin.

Jihar Borno ta dade tana fama da tashin hankalin dake da nasaba ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojin Nigeria ta ce kuma ta tsare wani da ake zargi nada hannu a tashin bam din.