Ana barna a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban rikon kwarya na CAR, Alexandre Nguendet

Wani rahoton hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya a kan rikicin jamhuriyar Afirka ta tsakiya, ya ce, bangarorin addinai sun yi ta kakkashe fararen hula, kuma an nakasa jama'a, tare da yin lalata da su.

A cewar masu binciken, mayakan Kirista na anti-Balaka sun kashe Musulmi masu yawa a watan Disamba, ciki har da mata da kananan yara.

Yayin da su kuma dakarun Seleka, Musulmi, suka hallaka Krista da yawa a matsayin ramuwa, ciki har da marasa lafiyar da ke kwance a asibiti.

A ranar Litinin mai zuwa kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar zai yi taron gaggawa, domin tattaunawa a kan lamarin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Karin bayani