Za'a ba Syria taimakon $400 miliyan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai 'yan gudun hijira fiye da miliyan hudu a Syria.

Kungiyoyin ci gaban al'umma dake taro a Kuwait sun yi alkawarin ba da agajin $400 miliyan ga Syria, kwana guda kafin wani taron kasashen duniya kan tallafawa Syria.

Za a yi amfani da kudin ne domin taimakawa 'yan gudun hijira da ke cikin matsi a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan Syria miliyan hudu ne suka kauracewa gidajensu tare da neman mafaka cikin kasar, yayin da karin mutane miliyan biyu suka fice daga kasar daga farkon yakin basasar da yanzu haka ke cikin wata na 35 da fara wa.

Karin bayani