Amurka ta soki wani ministan Isra'ila

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry

Amirka ta yi kakkausan suka dangane da wasu kalaman da aka ce ministan tsaron Isra'ila, Moshe Yaalon, ya yi.

A kalaman nasa Mr Yaalon din ya zargi sakataren tsaron Amirka, John Kerry, da gabatar da wani shirin kawo zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Isra'ila, wanda yake jin in ba shi ba, babu wani kamarsa.

A cewar wata kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amirkar, kalaman ba su dace ba, musamman ganin irin taimakon da Amirkar ke yiwa Isra'ilar ta fuskar tsaro.

Rahotanni sun kuma ambato ministan tsaron Isra'ilar, Moshe Yaalon yana cewa, shirin Mr Kerry dangane da tsaron Isra'ilar shirme ne kawai.

Karin bayani