Zakuna za su kare a Yammacin Afrika

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bunkasar noma na barazana ga zakuna a Yammacin Afrika

Wani sabon bincike ya gano cewa, zakuna zasu iya karewa a yammacin Afirka, inda a yanzu haka yawansu ya kasa 500.

Kungiyar Panthera ce ta kwashe fiye da shekaru shida ta na gudanar da binciken a kasashe 17, daga Senegal zuwa Nigeria.

In ji Panthera, yawan zakunan yayi matukar raguwa a Afirka ta yammar.

Ta ce a yanzu, yankin da suke kai-kawo, kashi daya ne kawai na yadda yake a da, saboda ayyukan noma.

Kungiyar ta ce ya kamata a sa zakunan na yammacin Afirka, a jerin dabbobin da ke fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa.