Rikicin CAR na ci gaba da jan hankula

Image caption An nemi kasashen duniya su kawo karshen rikicin CAR

Babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga kasashen duniya da su sanya hannu domin kawo karshen abinda ya kira rikici mai girma da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ke ciki.

Da yake magana da BBC a babban birnin kasar Bangui, John Ging da ke hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar yace al'umma na zaune cikin zullumi a kasar da kuma miliyoyin mutanen da suke tsananin bukatar abinci da muhalli da kuma magunguna.

Mr Ging ya kuma kara da cewa halin da mutanen kauyuka ke ciki ya munana.

Ya ce "Na kai ziyara wasu kauyuka da ke Bossangoa jiya, mutanen kauyen da ke da nesa da Bangui na matukar shan wahala. Da farko an ware su can gefe ne, kuma saboda wannan wariyar kayayyakin agaji basa isa garesu."

Ana dai samun raguwar tashe-tashen hankula tsakanin Musulmi da Kirista a Jamhuriyar Africa ta Tsakiyar a 'yan kwanakin nan, tun bayan da shugaban kasar Michel Djotodia ya sauka daga mulki.

Karin bayani