An yi wa 'yar Denmark fyade a India

Image caption 'Yan yawon bude ido na dabdala a Pahar Ganj, birnin Delhi

'Yan sanda a India na binciken fyaden da ake zargin an yi wa wata mai yawon bude ido 'yar Denmark a Delhi, babban birnin kasar.

'Yan daukar amarya sun kai wa matar mai shekaru 51 farmaki ne bayan da ta bata kusa da otal dinta a yankin 'yan yawon bude ido na Pahar Ganj.

'Yan sanda sun ce mutanen sun yi mata fashi da makami sannan su ka yi mata fyade, amma yanzu ta bar kasar.

A bara ne dai India ta tsananta dokokinta kan fyade bayan da wani gungun samari ya hallaka wata daliba ta hanyar fyade a birnin Delhi.

Sai di masu fafutuka na cewa har yanzu ana ci gaba da fyade da keta hakkin mata a India.

Karin bayani