Maiduguri: Mutane 30 bam ya hallaka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Motoci akalla 30 suka kone

Akalla mutane 30 ne suka mutu sannan wasu da dama suka samu raunuka sakamakon fashewar bam a wata mota a kusa da kasuwar jagwal dake Maiduguri babban birnin jihar Borno a Nigeria.

Wasu majiyoyi a asibitin Maiduguri sun tabbatar wa BBC cewar akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya karu, amma dai 'yan sanda sun ce mutane 19 ne suka rasu.

Kakakin soji a Maiduguri, Kanar Muhammed Dole ana shi bangaren bai bada adadin mutanen da suka rasu ba, amma ya ce motoci 10 da babura masu kafa uku sun kone sakamakon harin.

Wannan shine hari mafi muni da aka kai a cikin birnin Maiduguri cikin kusan watanni 10.

Shugaban kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal Jihad da ake kira Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi ikirarin cewa kungiyarsa ce ta kai harin na Maiduguri.

Gwamnatin jihar Borno ta bada umurnin a gudanar da bincike a kan lamarin.

Karin bayani