An soki Najeriya kan haramta auren jinsi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Navi ta yi kakkausar suka ga Najeriya kan haramta auren jinsi

Shugabar hukumar kula da hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ta yi kakkausar suka game da abinda ta kira sabuwar doka mai tsauri da ta haramta auren jinsi, da harkokin luwadi da madigo a Nigeria.

Navi Pillay, ta ce ba kasafai ta kan ga wata doka mai dan sakin layi kadan, da ta keta hakkokida dama na dan Adam kamar wacce aka zartar a Nigeria ba.

Ta kuma ce hukuncin zai iya tunzura abinda zai kawo rikici ko kuma nuna bambanci.

Shugaba Goodluck Jonathan dai ya rattaba hannu akan dokar haramta auren jinsi a farkon wannan watan, duk da cewa sai a kwanakin da suka gabata ne aka sanar da ita.

Haka kuma a karkashin dokar an tanadi daurin shekaru 14 a gidan kaso ga duk wanda ya shiga kungiyoyin masu auren jinsin guda da kuma daurin shekaru 10 ga duk wanda ya tallafa wa harkar.

Karin bayani