Ana taron bada agaji ga Syria a Kuwait

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikicin Syria na jefa mutane cikin yunwa

Kasashe masu bada tallafi na taro a Kuwait, inda Majalisar Dinkin Duniya ke neman gidauniyar $6.5 biliyan domin agaza wa wadanda rikicin Syria ya rutsa da su.

Wannan ce gidauniyar taimako mafi girma a tarihin majalisar.

Ana gudanar da taron ne yayin da ake samun rahotannin tsananin yunwa a yankunan da yakin ya hana kai dauki.

Kusan rabin al'ummar Syria na bukatar taimako.

Wata mai fafutuka a birnin Damscus Susan Ahmad ta shaidawa BBC cewa "a kullum muna samun wadanda suka mutu saboda tsananin yunwa, ko a jiya wata mata da 'ya'yanta sun mutu saboda sun ci abincin da ya lalace."

Karin bayani