An fara shari'ar harin Westgate a Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutanen hudu sun musanta zargin

An fara shari'ar mutane hudun da ake zargi da taimakawa maharan rukunin kantunan Westgate a Nairobi, babban birnin Kenya a watan Satumban da ya wuce.

Shaidu biyu sun bayyana gaban kotun kafin dage shari'ar zuwa ranar Alhamis.

Ana zargin mutanen hudu ne da taimakawa wadanda suka kai harin da ya hallaka mutane 67 tare da jikkata wasu 200.

Gaba dayansu dai sun musanta zargin.

Kungiyar al-Shabaab mai alaka da al-Qaeda ta ce ita ce ta kai harin.