Apple zai mayar wa iyaye N5.5 biliyan

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Yara kan sayi damar ci gaba a wasannin app store ba da sanin iyayesu ba.

Kamfanin Apple zai mayar wa da abokan huldarsa akallla $32.5miliyan (N5.5 biliyan) bayan da ya cimma yarjejeniya da hukumar cinikayya ta Amurka.

Yarjejeniyar ta kawo karshen korafe-korafen da iyaye ke yi game da sayayyar da 'ya'yansu ke yi a lokacin da suke buga wasanni a na'urorin Apple ba tare da amincewarsu ba.

An kuma bukaci Apple ya sauya yadda ya ke cire kudi daga asusun abokan huldarsa ta yadda zai tabbatar sun amince da sayayyar kafin ya caje su.

Kamfanin ya ce ya amince da sasantawar ne saboda bayan son ya shiga doguwar shari'a.

Shugabar hukumar cinikin ta Amurka, Edith Ramirez ta ce "Wannan yarjejeniyar nasara ce ga masu sayen kaya tare da gargadi ga sauran kamfanoni: ko ka na ciniki ta hanyar tafi-da-gidanka ne ko kuma a shagon gefen hanya, wajibi ne ka tsare hakkin abokan kasuwancinka."

Dubunnan korafe-korafe

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumar cinikin ta yi zargin cewa Apple ba ya sanar da iyaye cewa duk lokacin da su ka amince da sayen wani abu daga manhajar App Store, 'ya'yansu za su iya cigaba da sayayya tsawon minti 15 ba tare da neman tantancewa ba.

Haka kuma Apple ya kan bukaci masu amfani da na'urorinsa su bada kalmar amincewarsu ta sirri ba tare da bayyana musu hakan na nufin yarda da duk wani ciniki da aka yi ta cikin manhajar App Store ba.

Hukumar ta ce Apple ya karbi dubunnan korafe-korafe daga iyaye game da sayayyar da 'ya'yansu kan yi ba tare da saninsu ba.

Kan haka ne ta bai wa kamfanin wa'adin 31 ga Maris ya sauya tsarin cajin kudinsa ta yadda zai tabbatar iyaye sun amince kafin ya sayar wa da yara wani abu.

Alkawari

Apple dai ya ce tun bara ya fara kokarin mayar da kudin iyayen da 'ya'yansu suka yi sayayya ba da saninsu ba.

Ya ce: "Mun samu korafe-korafe 37,000 kuma zamu mayar wa da kowannensu kudinsa kamar yadda mu ka dau alkawari."

Manhajar App Store da ke cikin na'urorin Apple na kunshe da wasanni iri-iri na yara, inda mafi yawansu suke bada damar yin sayayya ta cikinsu.

Yawanci abubuwan da yaran ke saya kan ba su damar wucewa mataki na gaba ne a cikin wasannin.

Farashin abubuwan kan kama daga N150 zuwa N17,000.