Arangamar dakarun Najeriya da Boko Haram a iyakar Kamaru

Harkar tsaro a garin Banki kan iyakar Najeriya da Kamaru Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harkar tsaro a garin Banki kan iyakar Najeriya da Kamaru

Rahotanni sun ce an yi arangama tsakanin sojojin Najeriya da wasu 'yan kungiyar Boko Haram a garin Amchideh kan iyakarta da Kamaru.

Ana jin cewa mambobin wannan kungiyar sun shigo ne daga Najeriya, domin su kaiwa barikin 'yan sanda na garin Banki hari.

Rahotanni daga majiyoyin 'yan sanda sun ce an samu asarar rayukan jama'a daga bangaren fararen hula da kuma sojoji.

Garin na Amchideh da wuri ne na samun mafaka ga tarin 'yan gudun hijira daga jihar Borno a Najeriya, yanzu ya zama wani dandalin atisayen 'yan kungiyar Boko Haram don fafatawarsu da dakarun Najeriyar.

Bayan da dakarun Najeriyar suka fara kai musu farmaki da sama, membobin kungiyar ta boko haram sun sake tserewa zuwa garin Limami.

Duk da cewa 'yan kungiyar basu kai hari kan al'ummar Kamaru da sojojinta ba, musayar wutar da aka rika yi tsakanin bangarorin biyu ta kasa da ta sama ya kai ga jikkkata fararen hula daga bangaren Kamaru da lalata tarin dukiyoyi.