Gargagi kan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Hakkin mallakar hoto NA
Image caption Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Wani babban wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya yayi gargadin hatsarin da ke tattare da kisan kare dangi.

Jami'in Mr John Ging ya yi kira da kasashen duniya da su yi hobbasa wajen hana karin zubda jini.

Ya kuma ce rikicin tsakanin mayakan sa- kai masu gaba da juna na kama da wanda aka gani a wurare kamar Rwanda da Bosnia

Daruruwan musulmai ne aka yiwa rakiya zuwa kan iyakar kasar da makwabciyarta kasar Chadi, bayan barazanar da mayakan sa-kai Kiristoci ke yi musu.

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Mr Ging ya ce fargabar barazanar na kara mamaye zukatan tsakanin al'ummomin kasar.

Wani wakilin BBC a arewacin Kasar yace har yanzu akwai zaman dar- dar musamman a yankunan da ba' a jibge dakarun kiyaye zaman lafiya ba.