China ta kama malamin Musulunci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Musulmin China na fama da matsi daga gwamnati

'Yan sanda a Beijing sun kame fitaccen malamin Islama dan kabilar Uighur, Ilham Tohti.

Matar Mr Tohti, Guzaili Nu'er ta shaida wa manema labarai cewa fiye da 'yan sanda 24 ne suka kai hari gidansu ranar Laraba, inda suka yi awon gaba da mijinta, kwamfutoci, wayoyin tarho da kuma littattafai.

Ilham Tohti dai fitaccen mai sukar gwamnatin China ne.

A makonnin baya, an samu tashe-tashen hankula a Xinjiang - lardin yammacin China da mafi yawan mazaunansa Musulmi ne 'yan kabilar Uighur.

Karin bayani