An fara shari'ar kisan Rafik Hariri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani murgujejen bom ne ya kashe Rafik Hariri da mutane 20

Kotun hukunta masu manyan laifuka ta birnin Hague ta fara shari'ar mutane hudun da ake zarginsu da kashe tsohon Pirai ministan Lebanon, Rafik Hariri.

Ana dai shari'ar mutanen masu alaka da kungiyar Hezbollah ne ba tare da sun halarci kotun ba.

Wannan ne karo na farko da ake shari'ar wadanda ake zargi da aikata ta'addanci a kotun duniya.

Rafik Hariri na cikin mutane 21 da wani murkusheshen bom ya kashe a Beirut, Lebanon.

Bom din ya yi sanadiyyar rikici a Lebanon, wanda ya tilasta wa Syria janye dakarunta.

Hezbollah dai ta musanta cewa da hannunta a kai harin.