Garanbawul a bangaren tsaron Nigeria

Shugaba Goodluck Jonathan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya sallami hafsoshin dakarun kasar, kuma tuni ya nada sabbobbi.

Kakakin fadar shugaban kasar, Reuben Abati shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwar da ya aike wa manema labarai.

Sanarwar ta ce Air Mashal Alex Badeh, shi ne babban hafsan dakarun tsaron kasar inda ya maye gurbin Admiral Ola Sa'ad Ibrahim.

Manjo Janar, Keneth Tobiah Jacob shi ne sabon hafsan dakarun kasa inda maye gurbin Laftanar Janar Azubike O. Ihejirika.

Rear Admiral Usman O. Jibrin ya maye gurbin Vice Admiral Joseph Ezeoba a matsayin hafsan dakarun ruwan Nigeria sai kuma Air Vice Marshal Adesola Nunayon Amosu wanda ya maye gurbin Air Marshal Badeh a matsayin hafsan dakarun saman kasar.

Dukkan sauye-sauyen sun fara aiki nan take.

Masu sharhi na kallon sauyin a matsayin wata alama ta kokarin kawo karshen tabarbarewar tsaro a cikin Nigeria.