Motocin haya na yajin aiki a Nijar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yajin aikin ya tilasta wa mutane tafiya a kasa.

Direbobin motocin haya na yajin aikin yini guda a jamhuriyar Nijar domin nuna adawarsu da hauhawar farashin man fetur.

Rashin motocin hayis da tasi a titunan kasar dai ya kawo matukar tsaiko ga zirga-zirgar jama'a.

Gwamnatin kasar ta samar da wasu motocin sufuri domin sauwaka wahalar ga mazauna Niamey, babban birnin kasar amma dai ba su wadata ba.