PDP ta amince da saukar Bamanga Tukur

Hakkin mallakar hoto pdp website
Image caption Jam'iyyar PDP na fama da rikicin cikin gida

Majalisar zartarwar jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta amince da takardar murabus da shugaban jam'iyyar Alhaji Bamanga Tukur ya aike mata.

A ranar Laraba ne dai, Bamanga Tukur ya mika takardar murabus din bayan da a baya ya kafe cewa shi ba zai bar mukamin ba.

Rahotanni sun ce gwamnoni da shugabannin jam'iyyar na jihohi ne suka bukaci tsohon shugaban da ya ajiye aiki bisa zargin mulkin karfa-karfa.

Salon mulkin Bamanga Tukur na daya daga cikin dalilan da suka sa wasu gwamnoni biyar da 'yan majalisar wakilai 37 suka bar jam'iyyar a baya.

Rikicin cikin gida na jam'iyyar PDP ke fuskanta na da nasaba da batun wanda zai tsayawa jam'iyyar takara a zaben shugaban kasa a shekara ta 2015.

Wasu gwamnonin arewacin kasar sun yi zargin cewar Shugaba Jonathan a lokacin zaben 2011, ya dauki alkawarin yin wa'adin mulki daya ne, amma mukarrabansa sun musanta hakan.

Karin bayani