Dakarun Uganda na yaki a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Salva Kiir na Sudan ta Kudu da Yoweri Museveni na Uganda

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, ya ce dakarun kasarsa na taimakawa sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu a yakin da suke yi da 'yan tawaye.

Mr Museveni ya ce dakarun na Uganda da Sudan ta Kudu sun yi nasara kan 'yan tawayen a abinda ya kira kazamar arangama a wani wuri mai nisan kilomita 90 daga Juba, babban birnin Sudan ta Kudu.

Ya ce an kashe wasu daga cikin sojojin Ugandan.

Kakakin sojin Uganda ya ce an shaya daga ne a daura da garin Bor, wanda ke karkashin ikon 'yan tawayen.

Karin bayani