419 ya zama ruwan dare a Ivory Coast

419 ta hanyar intanet ya zama ruwan dare a Ivory Coast, abinda gwamnatin kasar ta ce tana kokarin magancewa.

A cewar gwamnatin, a watannin shidan farkon 2013 ta karbi kararrakin da suka danganci 419 fiye da kowacce kasa a Afrika.

A gabar kogin Ebrie dake tsakiyar birnin Abidjan, wani tsohon dan 419 da bai amince a bayyana sunansa ba ya ce ya fara ne yana shekara 16 saboda abinda ake yayi ke nan.

A yayin da matashin mai shekaru 22 yake kashe sigarin da yake zuka tare da waiwaya wa ya tabbatar babu mai jinsa, ya ce babu hanyar da tafi saurin kawo wuta kamar "soyayya."

"Ka samu mace ko namiji masu neman masoya ku fara hira da su ka aika musu hoto."

"Bayan nan sai ka ce ina ko son zuwa wurinka amma akwai wani bashi da ake bi na. Ko zaka aiko min da Euro 5,000 (N1,000,000)?"

Shi ke nan sai "masoyin" ya turo kudin daga nan sai ya nemi shi ya rasa.

Suwaga

Idan dawa ya yi nama su kan samu Euro 5,000 zuwa 12,000 (N1,000,000 zuwa N2,400,000).

To ko wane amfani ya ke da kudin da ya samu? "suwaga" "Ka gane? Mata, harka, kayan sawa, turare da sauransu."

Shekarun mafi yawan 'yan 419 na Ivory Coast ba sa wuce 16/17 kowanne kan samu Naira miliyan biyu a wata.

Sai dai masu harkar fasahar sadawarwa a Abidjan sun fara daukar martani kan wadannan bata gari.

Image caption Emmanuel Assouan, dagacin intanet na Abidjan

A bara ne aka zabi Emmanuel Assouan mai shekaru 22, a matsayin dagacin intanet na farko na Abidjan.

Dagacin kan koya wa matasa halattattun hanyoyin samun kudi ta intanet ne - misali tsara shafukan intanet ko kuma wallafa bayanai.

Sai dai abin da kamar wuya. Saboda 'yan 419 suka burge mutane a Ivory Coast sakamakon bushashar da suke da kudi.

A shekaru biyun da suka wuce, an kiyasta cewa sun damfari mutane daga sassa dabam daban na duniya sama da $15miliyan, wannan fa shi ne iyakar abinda 'yan sanda suka iya gano wa.

Cibiyar musamman

Shugaban hukumar leken asirin Ivory Coast, Stephane Konan ya ce kasarsa tafi kowacce a Afrika yawan masu damfara ta intanet saboda yafi fashi da makami saukin hatsari.

Kasar ta yi kaurin suna kan 419 amma kuma an yi mata shaidar kirki bisa kokarin magance matsalar.

Gwamnatin ta kafa wata cibiya ta musamman mai yaki da damfarar intanet, wacce ita ce ta farko irinta a Afrika.

Cibiyar na dakin bincike na zamani wanda ke iya gano mutanen da ke amfani da intanet koda sun batar da sunansu.

A bara sun kama mutane 100 tare da tallata sunansu, kuma sabuwar dokar aka zartar a watan Mayu ta bada damar daurin shekaru 20 ga 'yan 419.

Bayanan da suke tattarawa ta sa sun fahimci yadda 'yan damfarar ke gudanar da harkokinsu.

Ga misali sun gano cewa damfarar "soyayya" tafi yawa kuma fiye da rabin wadanda ake damfara a Ivory Coast sun fito ne daga France sai Ivory Coast, Belgium da Canada.

A can a gabar kogin Ebrie na tambayi tsohon dan damfarar ko ya na nadamar abinda ya yi.

Ya ce: "Lokacin da nake yi na kan ji ba dadi amma sai in tuna cewa neman kudi ne. Don haka ba na nadama."

Baya nadama amma kama shi sau biyu, tsoro ya sa ya bari. Yanzu ya na jami'a ya na karantar fasahar sadarwa.