Auren jinsi daya: Najeriya ta maida martani ga masu suka

Abba Moro Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Najeriya ta ce tana da tsarin dabi'unta da al'adun ta

A Najeriya, a karon farko hukumomin kasar sun fara maida martani ga sukar dake fitowa musamman daga kungiyoyi da wasu gwamnatoci na kasashen waje, game da matakin da gwamnatin Kasar ta dauka na kafa dokar haramta aure tsakanin masu jinsi iri daya.

Hukumomin na Nijeriya suka ce masu sukar lamirin wannan mataki suna yi ne don son zuciya, saboda addinai da al'adun 'yan Najeriyar baki-daya basu amince da wannan halayyar ba.

A wata hira ta musamman da BBC, Ministan cikin gida na Najeriyar Mr Abba Moro, ya ce Najeriya kasa ce mai 'yancin kanta kuma tana da tsarin al'adunta da kuma dabi'u.

'Ina ganin kamata yayi Amurka da Turai su mutunta Najeriya saboda kiyayewar da tayi da al'adun mutanen ta' a cewar Minista Abba Moro.